Home / Labarai / Rundunar ‘Yansandan Jihar Yobe Tayi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yiwa Wani Matashi

Rundunar ‘Yansandan Jihar Yobe Tayi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yiwa Wani Matashi

Rundunar 'Yansandan Jihar Yobe Tayi Allah-Wadai Da Kisan Killar Da Aka Yiwa Wani Matashi                Daga Bello Usman.

 

 

Rundunar ‘Yansandan jihar Yobe tayi Allah-Wadai, da kisan da aka yiwa wani Matashi me suna Lawan Adamu, ɗan kimanin shekaru 28 da haihuwa.

Kakakin rundunar na jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA, inda ya ce an yasar da gawar Matashin ne a bayan garin Nayi-Nawa na birnin Damaturu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, da misalin ƙarfe 10:30 na daren Lahadin da ta gabata ne, aka sanarwa Shelkwatar ‘yansandan cewa ga wata Gawa ɗauke da raunuka.

A cewar Dungus “Bayan Jami’anmu sunje sai suka iske Mutumin an yanka masa maƙogwaro dama sauran raunuka a jikinsa, baya ga wata wuƙa ɗauke da jini da aka gani a wurin”.

Kuma bayan ai kai shi Asibitin Ƙwararru dake Birnin Damaturu Likitoci suka tabbatar da rasuwar sa, adan haka aka ajiye gawar a ɗakin ajiyar Gawarwaki.

Toh sai dai tuni rundunar ta sami nasarar kama wanda ake zargi da kisan gillar, me suna Yunusa Isa (Abba) a wurin da aka iske gawar.

Adan haka ne Kwamishinan ‘Yansandan jihar CP Garba Ahmed, ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin kisan, harma ya bawa al’umma tabbacin yin adalci a yayin binciken kamar yadda doka ta tanada.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar