Daga Bashir Gasau.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta sami nasarar kama wani korarren Soja, dake karɓar Kuɗi a hannun Mutane da sunan zai yi musu hanyar samun aiki.
Kakakin rundunar a jihar Bauchi, SP Ahmed Muhammed Wakil ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya ce sun kama shi ne bayan ƙorafin da wasu Mutane Uku suka shigar a kansa.
A cewar SP Wakil “Mun sami nasarar kama korarren Sojan Aliyu Adamu ɗan asalin ƙaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa, bisa zargin sa da laifuka huɗu waɗanda suka haɗar da Sojan gona, cuta, laifin Almubazzaranci da kuma zamba cikin aminci”.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya karɓi Kuɗi Naira Dubu ɗari Biyu a wurin masu ƙorafin, bisa alƙawarin zai samar musu aikin a rundunar Sojin Najeriya, amma kuma sai suka ji shuru ba’a kira su domin fara karɓar horon aikin ba.
Toh sai dai tuni Korarren Sojan me muƙamin ƙaramin Kofral (Lance Corporal), ya amsa laifin sa na karɓar Kuɗin masu ƙorafin kuma ya je ya biya buƙatun sa dasu.
Haka kuma ya tabbatar wa da ‘yan Sandan cewa an kore shi a watannin baya saboda fashin zuwa wajen aiki na shekara guda ba tare da samun izini ba.
Adan haka ne Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar CP Auwal Musa Mohammed, ya bada tabbacin gurfanar da shi a gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.
A ƙarshe ya shawarci al’umma da su dinga kula da irin waɗannan ‘yan damfara da sunan samar musu aiki, harma ya ce su dinga kai rahotannin su ga hukuma mafi kusa.