Daga Bashir Gasau.
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sauke shugabanin riƙo na ƙananan hukumomin jihar 44 nan take.
Gwamnan ya bada umarnin ne yayin taro na musamman da ya yi da shugabannin riƙon a gidan gwamnatin jihar, inda ya ce saukewar ya haɗa da mataimakan shugabannin ƙananan hukumomin, sakatarori da kuma Kansiloli na kowacce ƙaramar hukuma.
Gwamnan ya kuma umarce su da su miƙa jagorancin ƙananan hukumomin ga daraktocin mulki na kowacce ƙaramar hukuma.
Haka kuma ya gode musu a bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci-gaban yankunansu, tare da jaddada cewa gwamnati zata ci-gaba da tafiya dasu a guraben da suka dace.
A nasu ɓangaren, shugabannin rikon sun godewa gwamna Abba Kabir Yusuf, dangane da wannan dama da ya basu na hidimtawa al’ummar su na tsawon wannan lokaci.