Home / Labarai / Hukumar Kula Da Gidajen Gyaran Hali Ta Kano Tayi Sabon Shugaba

Hukumar Kula Da Gidajen Gyaran Hali Ta Kano Tayi Sabon Shugaba

Hukumar Kula Da Gidajen Gyaran Hali Ta Kano Tayi Sabon Shugaba              Daga Bashir Gasau.

 

Sabon Kwanturolan hukumar dake kula da gidajen gyaran hali na ƙasa reshen jihar Kano, Ado Inuwa, ya buƙaci haɗin kan abokan aikin sa dama dukkan al’ummar jihar domin aikin hukumar ya tafi cikin nasara.

Kwanturolan ya buƙaci hakan ne a yayin da yake jawabin kama aiki a matsayin Shugaban Hukumar na kano, bayan ya karɓi ragamar kama aikin daga hannun tsohon Kwanturolan Sulaiman Muhammad Inuwa, wanda yayi ritaya bayan cikarsa shekaru 35 da fara aiki.

Inuwa ya yabawa Jami’an hukumar a bisa Kyakykyawar tarbar da suka yi masa, harma ya yi kira a garesu da su bashi haɗin kai, wajen taimakon ɗaurarrun dake gidajen dama masu jiran hukunci.

A ƙarshe sanarwar Kakakin hukumar na Kano, SC Musbahu lawan ƙofar Nasarawa ta ce, sabon Shugaban ya buƙaci haɗin kan sauran Hukumomin tsaron dake jihar domin ƙara inganta tsaron a lungu da saƙo.

Kafin zuwan sabon Kwanturolan jihar Kano dai, ya kasance Shugaban Hukumar na jihar Jigawa.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar