Home / Flooding / Jihohin Najeriya 11 Su Shiryawa Ambaliya Saboda Sako Ruwan Dam Ɗin Kamaru

Jihohin Najeriya 11 Su Shiryawa Ambaliya Saboda Sako Ruwan Dam Ɗin Kamaru

Jihohin Najeriya 11 Su Shiryawa Ambaliya Saboda Sako Ruwan Dam Ɗin Kamaru             Daga Bello Usman.

 

 

Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ƴan ƙasar da su kasance cikin shirin shigowar ruwa daga dam ɗin Lagdo na ƙasar Kamaru.

Darakta-Janar na Hukumar Albarkatun Ruwa ta Najeriya (NIHSA), Umar Mohammed, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Sai dai ya buƙaci ƴan Najeriya su kwantar da hankalinsu, inda ya ce ba za’a samu mummunar ambaliya ba a Najeriya saboda buɗe dam ɗin.

Sai dai ya ƙara da cewa jihohin Adamawa da Taraba da Kogi da Nasarawa da Benue da Anambra da Bayelsa da Delta da Edo da Kuros Riba da Rivers suna buƙatar fara shirin ko ta kwana domin rage illar ambaliyar idan ta auku.

Wata ƙididdiga daga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta nuna cewa da aka sako ruwan Dam ɗin ne girman 586 km2 a shekarar 2022, ya jawo mummunar ambaliya, inda mutum 603 suka mutu, sannan sama da mutum miliyan 1.4 suka rasa muhallansu, sannan wasu 2,400 suka jikkata.

Haka ambaliyar ta 2022 ta ɓarnata gidaje 82,035 da hekta 332,327 na gonaki.

Awatan Oktoban 2023 ne Majalisar Dattawa ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta waiwayi batun gina madatsar ruwa na Dasin Hausa da sauransu, domin su riƙa tare ruwan dam ɗin na Lagdo dake ƙasar Kamaru idan ya malalo.

Daily Trust.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar