Home / Government / Kansar Ƙwaƙwalwa : Gwamnan Bauchi Ya Tallafawa ‘Yar Jarida Domin Neman Lafiyar Ta

Kansar Ƙwaƙwalwa : Gwamnan Bauchi Ya Tallafawa ‘Yar Jarida Domin Neman Lafiyar Ta

Kansar Ƙwaƙwalwa : Gwamnan Bauchi Ya Tallafawa 'Yar Jarida Domin Neman Lafiyar Ta             Daga Bashir Gasau.

 

A ƙoƙarin sa na nuna tausayi da shugabanci na gari, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bada tallafin Naira Milyan 5 ga wata ‘yar jarida, domin jiyyar ta akan lalurar Kansar Ƙwaƙwalwa a Asibitin Ƙwararru na Jami’ar Jos dake jihar Plateau.

Mai bawa Gwamnan shawara kan yaɗa labarai Kwamared Mukhtar Giɗaɗo ne ya miƙa Cakin Kuɗin a madadin Gwamnan, inda ya bayyana Gwamnan a matsayin wanda yake sadaukar da kansa wajen rage wahalhalun da ‘yan ƙasa suke ciki.

Haka kuma Giɗaɗo ya ce gudunmawar farko da aka bayar ta Naira Milyan 1.3, ta ƙara nuna jajircewar Gwamnan wajen ganin Hafsat ta sami lafiya.

A nasa ɓangaren Shugaban Ƙungiyar Gidajen Jaridu (Correspondent Chapel), na jihar Bauchi, Ahmed Muhammed ya godewa Gwamnan dama Mashawacin sa a bisa halin nagarta da suka nuna, harma ya bayyana shirin ƙungiyar tasu na ci-gaba da bawa Gwamnatin goyon baya domin cimma abubuwan da aka sanya a gaba.

Sanarwar da Mashawacin Gwamnan akan kafafen sada zumunta, Alhaji Nuru Abdullahi (Baban Zarah), ya aiko wa jaridar GTR HAUSA ta ce tallafin ya faranta ran al’umma, duba da ya ƙara futo da yunƙurin Gwamnatin na kyautata rayuwar ‘yan ƙasa.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar