Home / Government / Tiriliyan 1.2 Aka Raba Tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Ƙananan Hukumomi – FAAC

Tiriliyan 1.2 Aka Raba Tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Ƙananan Hukumomi – FAAC

Tiriliyan 1.2 Aka Raba Tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Ƙananan Hukumomi - FAAC             Daga Bello Usman.

 

Kwamitin Rarraba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC), ya ce ya raba naira tiriliyan 1.2 ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihohi dama na ƙananan Hukumomi, bayan samun Kuɗin ta hanyar Kuɗin shigan watan Agustan 2024

An raba Kuɗin ne a lokacin taron FAAC na watan Satumba 2024 da aka gudanar a Abuja, kamar yadda sanarwar da Daraktan yaɗa Labaran da Hulɗa da Jama’a na Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Bawa Mokwa, ya fitar ta bayyana a jiya Talata.

Adadin kuɗin da aka raba ya nuna cewa raguwa kuɗin yayi da kashi 11 cikin 100 ko kuma naira Bilyan 155 daga naira tiriliyan 1.358 da aka raba a watan Yulin da ya gabata.

Bawa Mokwa ya ce kuɗin ya haɗa da kuɗin shiga na naira Bilyan 186.636, da kuma naira Bilyan 533.895 daga harajin VAT, naira Bilyan 15.02 daga harajin mu’amalar kuɗi ta intanet, da kuma naira Bilyan 468.25 daga bambancin da aka samu na canjin kuɗaɗe.

Bawa ya ƙara da cewa daga cikin jimillar naira tiriliyan 1,203 da aka raba, Gwamnatin Tarayya ta samu naira Bilyan 374,93, jihohi kuma sun samu naira Bilyan 422,86, yayin da ƙananan hukumomi suka samu naira Bilyan 306,53.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar