Home / Health / Amai Da Gudawa : Muna Bukatar Ƙarin Ma’aikata A Asibitin Wudil – Kwamitin Karta-kwana

Amai Da Gudawa : Muna Bukatar Ƙarin Ma’aikata A Asibitin Wudil – Kwamitin Karta-kwana

Amai Da Gudawa : Muna Bukatar Ƙarin Ma’aikata A Asibitin Wudil - Kwamitin Karta-kwana          Daga Bello Usman.

 

 

Kwamitin karta-kwana kan lura da harkokin lafiya a ƙaramar hukumar Wudil, ya bukaci ƙaramar hukumar da ta gaggauta samar da ƙarin ma’aikatan lafiya, wadanda zasu taimaka wajen lura da lafiyar masu cutar Amai da Gudawa a babban asibitin kwanciya na Wudil.

Ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin, kuma wakilin babban asibitin Wudil, Malam Adamu Usaini ne yayi kiran a yayin zaman da kwamitin yayi, inda ya ce yanzu haka yawan masu cutar amai da gudawar na sake ƙaruwa a kullum.

Malam Adamu wanda shine me lura da ɓangaren cututtuka na asibitin, ya ce rashin isassun ma’aikatan lafiyar yasa aikin na ƙara rincaɓe musu.

Sanarwar a jami’in yada labaran shiyyar Wudil Nasiru Habu Faragai ya aikowa jaridar GTR Hausa ta kara da cewa, akwai buƙatar ganin an kewaye ɓangaren da masu cutar suke, domin kaucewa kamuwar wasu mutanen da basu ji ba kuma basu gani ba.

Da yake jawabi daraktan ma’aikatan ƙaramar hukumar Alhaji Ismaila Tajo Gaya, ya bayyana cewa nan bada jimawa ba ƙaramar hukumar zata rarraba magunguna ga ƙananan asibitocin yankin, dan inganta ƙudirin gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf na inganta lafiyar al’umma.

A nasa jawabi tunda farko shugaban sashin ma’aikatar lafiya na ƙaramar hukumar Alhaji Bashir Usman yace maƙasudin kiran taron nasu shine, biyo bayan ɓullar cutar amai da gudawa a ƙaramar hukumar wadda tayi ajalin mutum guda, a yayin da mutum 26 suke samun kulawar gaggawa.

A karshe wakilin Hakimin yankin Alhaji Sunusi Sabo, ya umarci dagatai da masu unguwanni dama limamai su ci-gaba da wayar da kan jama’a, a masallatai da sauran guraren haɗuwar mutane domin kaucewa kamuwa da cutar.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar