Daga Bashir Gasau.
Gwamnatin jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum, ta fitar da Jadawalin waɗanda suka bada tallafin tallafi, akan iftila’in ambaliyar da ta faru a birnin Maiduguri.
Mashawacin Gwamnan akan yaɗa labarai Abdurrahman Ahmed Bundi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce zasu dinga sanar da ci-gaban da aka samu da misalin ƙarfe 7 na daren kowacce rana.
Ɓangarorin da suka bada tallafin ga waɗanda iftila’in ya shafa sun haɗar da manyan ‘yan kasuwa, Gwamnatin Jihohi, ‘yan Majalisar dokokin jihar dana tarayyar Najeriya, Ɗaiɗaikun Mutane, da kuma Ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Jihohi;
1. Bauchi = Naira Milyan 250
2. Kebbi = Naira Milyan 200
3. Adamawa = Naira Milyan 50
4. Yobe = Naira Milyan 100
5. Kano = Naira Milyan 100
6. Gombe = Naira Milyan 100
7. Taraba = Naira Milyan 100
8. Katsina = Naira Milyan 100
Ƙungiyoyi da Ɗaiɗaikun Mutane;
1. Alhaji Aliko Dangote = Naira Bilyan 2 (Bilyan 1 ga hukumar NEMA)
2. Alhaji Aminu Dantata = Naira Bilyan 1.5
3. HE Atiku Abubakar = Naira Milyan 100
4. HE Peter Obi = Naira Milyan 50
5. Hukumar bunƙasa yankin Arewa maso gabas = Naira Bilyan 3
6. Sanatocin Najeriya = Naira Milyan 54.5
7. Majalisar wakilan Najeriya = Naira Milyan 100
8. Jam’iyyar PDP = Naira Milyan 25
9. ‘Yan Majalisar dokokin jihar Borno = Naira Milyan 60
10. Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan = Naira Milyan 50
11. Honarabul Zainab Gimba = Naira Bilyan 25
12. Ibrahim Abba Umar = Naira Milyan 50
13. Sumaila Satumari = Naira Milyan 20
14. Honarabul Malam Gana Kareto = Naira Milyan 10
15. Ƙungiyar Sanatocin Arewaci = Naira Milyan 10
16. Sanata Barau Jibrin = Naira Milyan 10
17. Honarabul Moh’d Abubakar Maifata = Naira Milyan 50
18. ‘Yan Kudancin Borno = Naira Milyan 200
19. Honarabul Zakariya Dikwa = Naira Milyan 10
20. Al-Amanah Aid = Naira Milyan 1
21. Honarabul Mohammed Imam = Naira Milyan 50
22. HE Maina Ma’aji Lawan = Naira Milyan 10
23. HE Ali Modu Sheriff = Naira Milyan 100
24. Honarabul Dakta Ali Bukar Dalori = Naira Milyan 50
25. Sanata MT Monguno = Naira Milyan 50
26. Sanata Kaka Shehu Lawan = Naira Milyan 50
27. Honarabul Aliyu Betara = Naira Milyan 100
28. Honarabul Abdulkadir Rahis = Naira Milyan 25
29. Honarabul Ibrahim Abuna = Naira Milyan 25
30. Honarabul Usman Zannah = Naira Milyan 10
31. Honarabul Injiniya Bukar Talb = Naira Milyan 10
32. Honarabul Yerima Lawan Kareto = Naira Milyan 2
33. Abdussalam Kachallah = Naira Milyan 100
34. Awari Usman Alkali = Naira Milyan 20
35. Eighteenth Engineering Company (EEC) = Naira Milyan 50
36. Dan Nene Construction Company = Naira Milyan 30
37. Matar Shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu = Naira Milyan 500
38. Dauda Kahutu (Rarara) = Naira Milyan 10
39. Ƙananan Hukumomin jihar Borno = Naira Bilyan 1.350
40. Ƙungiyar Injiniyoyi ta ƙasa (NSE) da Majalisar dake tantance Injiniyoyi (COREN) = Naira Milyan 10
Waɗanda Suka Bada Tallafin Kaya;
1. Hukumar bunƙasa yankin Arewa maso gabas = Shinkafa me kilo 25 Buhu dubu 20, Macaroni Katon dubu 20, Galan ɗin Man Gyaɗa dubu 10.
2. Sumal Food Group, Ibadan = Buredi dubu 50 da Biskit Katon dubu 5.
3. Gwamnatin jihar Nasarawa = Shinkafa mota biyu, Spaghetti mota biyu da kuma Sukari mota biyu
4. General Buba Marwa (Rtd) = Takin Zamani mota 10, wanda kuɗin sa ya kai Naira Milyan 120
5. Honarabul Aminu Jaji (HOR) = Shinkafa Buhu 600
6. Ƙungiyar Injiniyoyi ta jihar Borno = wrappers dubu 10
7. Engineer Usman Monguno = wrappers dubu 10
8. Alhaji Abdulkadir Ali (Matrix Energy) = Kayan Abinci na Naira Milyan 120
9. National Agency for Great Green Wall =
Shinkafa kilo 25 guda 80, Man Gyaɗa 4.5 guda 30, Macaroni Katon 30, Spaghetti Katon 30, Rishon me amfani da Kalanzir guda 60, Manyan Tukwane 73, Tabarma 180, Kujerun Roba 175, Bokitin Roba 600, Kwanuka 578, Turmi da Taɓarya 78, Tabarmar Sallah 32, ƙananan Tabarmi 100, Rabobi da da manyan Farantan Roba 250, Takalmin wanka 256, Kofin Roba 700, ƙananan Farantan Roba 409, Butar Alwala 291, Tawul 96 da kuma Cokula 433.
10. Ƙungiyar Injiniyoyi ta ƙasa (NSE) da Majalisar dake tantance Injiniyoyi (COREN) = Kilo 400 na kayan Sawa.