Daga Bashir Gasau.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Kwamishina CP ML Yusufu, ba bawa al’ummar jihar wasu shawarwari biyo bayan faruwar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri.
Jami’n dake kula da masu magana da yawun Rundunar a Arewa maso gabas, SP Ahmed Mohammed Wakil ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa jaridar GTR Hausa, inda ya ce shawarwarin suna da matuƙar muhimmmanci a wannan hali da ake ciki.
Wakil ya ƙara da cewa rundunar tayi haɗin gwuiwa da sauran hukumomi domin tabbatar da doka da oda, ta hanyar kare lafiyar al’umma, hana ayyukan ɓata-gari, dama ci-gaba da ceto al’ummar da iftila’in ya shafa.
Shawarwarin dai sun haɗar da al’umma su ci-gaba da sanya idanu akan shige da ficen mutane, dama kai rahoton abinda basu gamsu da shi ba.
Sai ƙauracewa shiga yankunan da ambaliyar ta shafa, gudun kamuwa da cututtukan da ake iya ɗauka a ruwa dama sauran hadarurrika.
Bugu da ƙari da wayar da kan al’umma akan hanyoyin yin kandagarkin satar kayansu, dama bawa masu bada agajin gaggawa cikakken haɗin kai, a yayin gudanar da ayyukansu na Jin-ƙai.
Sai shawara ta ƙarshe tabbatar da sahihancin labari kafin a yaɗa shi, domin gudun yaɗa labaran ƙarya.
A karshe rundunar ta shawarci al’umma da su dinga sanar da su dukkan wani lamari na gaggawa akan waɗannan lambabi 080 68 07 55 81 ko 080 23 47 32 93, domin su kawo ɗauki.