Daga Aliyu Gerengi, Gombe.
Allah yayi wa Shahararren ɗan jaridar nan Ahmad Isah Koko rasuwa.
Malam Ahmad Koko, ya rasu ne a yau Alhamis bayan fama da jiyya, yayin da ake sa ran gudanar da jana’izarsa a gobe Juma’a.
Kafin rasuwar Ɗan Jaridar dai ya shahara wajen karanta littattafan Hausa a gidajen rediyo a ciki da wajen Najeriya.
Haka kuma karatun nasa yana matuƙar jan hankalin Mata da Matasa, duba da yadda yake sarrafa muryarsa domin yin muryoyin jinsin Mutane a mataki daban-daban.
Bugu da ƙari ya kasance tsohon ma’aikacin Rediyo Najeriya, kuma tsohon shugaban Sashen Hausa na Bond FM.
Da fatan Allah ya jiƙansa ya rahamshe, ya kuma bawa dukkan ‘yan uwa da abokan arziƙi haƙurin wannan rashi.