Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja.
Hukumar bayar da agajin Shari’a kyauta ta Najeriya wato (Legal Aid Council), ta sha alwashin ci-gaba da aiwatar da ayyukan ta na ƙwato haƙƙin waɗanda shari’ar su ke nuƙusani ba tare da wani dalili Mai ƙarfi ba.
Shugaban hukumar na Najeriya Barista Aliyu Abukabakar Gwandu ne ya sanar da hakan, a yayin zantawarsa da Jaridar GTR Hausa a ofishinsa dake babban birnin tarayya Abuja.
Barista Gwandu ya ƙara da cewa, babban aikin da ya rataya a wuyan hukumar sa shine, taimakon wanda duk aka yiwa ba dai-dai ba har lamarin ya kai ga kuliya manta Sabo, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Inda ya buƙaci al’ummar Najeriya da kada suyi ƙasa a gwuiwa, wajen miƙa kokensu a ɗaya daga cikin rassan ofisoshinsu dake jihohin Najeriya 36, haɗi da Abuja fadar mulkin ƙasar.
A cewar sa “Abubuwan da muke bada agajin gaggawa sun haɗar da rage cunkuso a gidan kaso, kai ziyara gidajen gyara hali da dai sauran ayyukan jin-ƙai.
A ƙarshe ya jaddada cewa hukumar su na iya tsayawa ‘Yan ƙasar dake da buƙatar agajin shari’a, duk akan wanda ya kama ba tare da an biya ko sisin kobo ba.