Home / Judiciary / Zargin Badaƙalar Filaye : Mun Ladabtar Da Magatakardar Kotuna Biyu – JSC Kano

Zargin Badaƙalar Filaye : Mun Ladabtar Da Magatakardar Kotuna Biyu – JSC Kano

Zargin Badaƙalar Filaye : Mun Ladabtar Da Magatakardar Kotuna Biyu - JSC Kano         Daga Bashir Gasau.

 

Hukumar kula da harkokin Shari’a ta jihar Kano (JSC), ta ladabtar da wasu Magatakardar Kotunan Shari’ar Musulunci Guda biyu

Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa a daren jiya, inda ya ce an ladabtar dasu ne bisa zargin badaƙalar Filaye.

Ɗaukar matakin ya zo ne a yayin taron hukumar karo na 75 da aka gudanar a ranar 12 ga watan Satumbar nan da muke ciki, bayan kwamitin bincike da aka kafa kan ƙorafin da akayi a kansu ya miƙa rahoton sa.

Kuma binciken ya gano cewa Jamilu Ibrahim tare da waɗanda suka haɗa baki sun karɓi kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba, ta hanyar bayar da takardar mallakar fili ta hanyar yaudara, domin siyar da filaye guda biyu.

Hakan ce tasa kwamitin ya bada shawarar a kori Jamilu Ibrahim daga aiki, amma hukumar shari’a ta dakatar da shi ba tare da biyan albashi ba har sai an kammala shari’ar da yake fuskanta a gaban kotun majistiri.

Shi Kuma Zubairu Sulaiman, wanda magatakardan Babbar Kotun Shari’a ne, an same shi da karɓar Naira miliyan ɗaya ta asusun sa na ƙashin kansa a matsayin la’ada bayan siyar da filayen guda biyu.

Adan haka ne shima Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta dakatar dashi na tsawon watanni huɗu ba tare da biyan albashi ba, kamar yadda kwamitin binciken ya bada shawara.

A ƙarshe hukumar ta jaddada aniyar ta na tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da takunkumin da ya dace, kan duk wani ma’aikaci da ya aikata ba dai-dai ba musamman waɗanda aka ɗora wa alhakin gudanar da shari’a, don kare mutunci da riƙon amanar ɓangaren shari’a dama tabbatar da amincewar jama’a.

 

 

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar