Daga Idris Alhassan Rijiyar Lemo.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Abdullahi Ibni Abbas (Kandahar) dake Rijiyar Lemo ta Jihar Kano, Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemo, ya shawarci talakawan Najeriya da su duƙufa da addu’a domin Allah ya cire su daga halin ƙuncin da suke ciki.
Shehin Malamin na bada wannan shawara ne a yayin huɗubar Sallar Jumu’a ta jiya Jumu’a, inda ya ce hakan shine dai-dai maimakon kausasa harshe da la’antar shugabanni, kan halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki na yunwa, fatara da kuma tsadar rayuwa.
Limamin wanda shine tsohon Kwamishinan Shari’a na jihar Kano ya ƙara da cewa, ya kamata su ƙara maida hankali wajen yawaita addu’o’i a koda yaushe.
A cewar sa “Ba’a yin addu’a da ra’ayi ko ganin dama, sai dai ayi ta da niyyar ibadah da neman ɗauki a wajen Allah, mai yaye kowacce irin damuwa ga bayinsa.
Adan haka ya ce wannan ne lokaci mafi dacewa da yin addu’o’in neman taimakon ubangiji, kan salon kamun ludayin shugabancin da ake yiwa Talakawa a wannan ƙasa da sauran matsalolin da suka dabai-baye ta.
A karshe tsohon kwamishinan ya ja hankalin al’umma da suke zaɓar nagartattun mutane wajen neman taimakon addu’ar su, a maimakon zuwa wajen waɗanda za su jefa su a hallaka ta hanyar raba su da imaninsu.