Daga Mukhtar Haliru Tambuwal.
Mai Girma Jarman Sokoto Dakta Ummarun Kwabo (Uban Marayu), da kuma Ɗan iyan Jarma Alhaji Murtala Abdul Ƙadir, sun bada tallafin kayan abinci na sama da Naira Milyan 30 ga waɗanda Iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugurin Jihar Borno.
Sadaukin Sokoto Malam Muhammad Lawal Maidoki, da kuma Shugaban Hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sokoto ne suka jagoranci kai kayan a madadin su, inda suka isar dasu ga Fadar Shehun Borno, Mai Martaba Alhaji Dakta Abubakar ibn Umar Garba El-kanemi.
Kayan da suka kai tallafin sun haɗar da;
1.Buhun Shinkafa me kilo 100 guda 100
2. Buhun Gari me kilo 100 guda 100
3. Katon ɗin Taliyar Spagetti guda 100
4. Maggi Katon 100
5. Jarkar Mai Guda 30
Da yake jawabi Shehun Borno, Mai Martaba Alhaji Dakta Abubakar ibn Umar Garba El-kanemi, ya yi addu’a ta musamman ga wadanda suka bayar da kayan, da kuma godiya a madadin Gwamnatin jihar, masarautar dama ɗaukacin Al’ummar jihar ta Borno.
Jarman Sokoto dai sanannen Ɗan Kasuwa ne kuma Ɗan Siyasa Mai taimakon Al’umma a jihar Sokoto, a inda shima Ɗan Iyan Jarma ya kasance na hannun daman sa wanda kuma yake taimakawa Alumma.