Home / Labarai / Attahiru Bafarawa : An Ƙaddamar Da Kwamitin Rabon Naira Bilyan Guda Ga Sakkwatawa

Attahiru Bafarawa : An Ƙaddamar Da Kwamitin Rabon Naira Bilyan Guda Ga Sakkwatawa

Attahiru Bafarawa : An Ƙaddamar Da Kwamitin Rabon Naira Bilyan Guda Ga Sakkwatawa    Daga Mukhtar Haliru Tambuwal.

 

Gidauniyar tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Dakta Attahiru Bafarawa, ta ƙaddamar da kwamitin da zai jagoranci rabon tallafin Naira Bilyan guda ga Sakkwatawan dake faɗin jihar.

Tsohon Gwamnan Jihar Dakta Attahiru Bafarawa ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin, inda ya ce ya bada tallafi ga mutanen jihar ne domin rage musu raɗaɗin talaucin da suke ciki.

Haka kuma ya jaddada godiyar sa ga al’ummar jihar a bisa damar da suka bashi, adan haka yayi alƙawarin ci-gaba da hidimta musu har abada.

A cewar Bafarawa “Wasu zasu kira wannan a matsayin neman afuwa amma nafi son a dubi rama alheri ne da alheri, na soyayyar da aka nuna min kuma yanzu ne yafi da cewa na rama duba da yadda jama’a ke cikin halin matsi”.

Da ya juya kan kwamitin da ya ƙaddamar, wanda shugaban hukumar Zakka da waƙafi na jihar Injiniya Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato) zai jagoranta, ya ce zaiyi aikin zaƙulo buƙatun Alummar Jihar domin samun sauƙin ayyukan.

Harma ya ce ya amince da rikon amanar sa kuma sananne ne a wurin gudanar da irin waɗannan ayyukan na Jin-ƙan al’umma da yiwa Addini Hidima.

A nasa ɓangaren Shugaban Kwamitin Injiniya Malam Muhammad Lawal Maidoki ya ce ƙofar su a buɗe take domin karɓar shawarwari, harma ya buƙaci Addu’ar al’umma domin samun nasarar aikin.

Shirin tallafin zai zagaye dukkan ƙananan hukumomin jihar ta Sokoto, inda za’a mayar da hankali wajen samar da abinci, ruwan sha da kuma suttura ga mutanen Jihar.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar