Home / Education / Iƙirarin Gwamnatin kano Kan Batun Ilimi Bada Gaske Bane – Ɗan Azumi Gwarzo

Iƙirarin Gwamnatin kano Kan Batun Ilimi Bada Gaske Bane – Ɗan Azumi Gwarzo

Iƙirarin Gwamnatin kano Kan Batun Ilimi Bada Gaske Bane - Ɗan Azumi Gwarzo       Daga Sani Ɗan Bala Gwarzo.

 

Tsohon Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Kano, Honarabul Ibrahim Ɗan Azumi Gwarzo, ya ce iƙirarin da Gwamnatin jihar ke yi akan batun Ilimi ba da gaske take ba.

Ɗan Azumi Gwarzo na wannan bayani ne biyo bayan matakin da Gwamnatin Kano ta ɗauka, akan Makarantar Sa’adatu Rimi na maida ita Kwaleji daga Jami’a, inda ya ce ko ma baya ga ɓangaran ilimi da ma Ɗaliban da suke Karatu a Makarantar.

A cewar tsohon Kwamishinan na Gwamnatin Ganduje da ta gabata “Makarantar ta cika duk wasu sharuɗɗa na zama Jami’a, duba da yadda hukumar kula da jami’oi ta ƙasa ta tantance tare da bada shedar fara karatun digiri”.

Bugu da ƙari yace gwamnatin ganduje tayi duk mai yiwuwa wajen samar da gine-gine, da kayan aikin da zasu tallafawa makarantar ta zama Jami’a, domin Ɗalibai su riƙa karatun digiri maimakon samun takardar shaidar koyarwa wato (NCE) kaɗai.

Adan haka ne ya ce Gwamnatin kano ba ta shiryawa ɓangaran ilimin ba, tunda ba da gaske take ba.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar