Home / Labarai / Zaɓen Kananan Hukumomi : Albishir Ga Waɗanda Suka Ajiye Muƙamansu Domin Takara A NNPP

Zaɓen Kananan Hukumomi : Albishir Ga Waɗanda Suka Ajiye Muƙamansu Domin Takara A NNPP

Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Kano Ta Bada Tallafin Naira Milyan Ɗari Ga Waɗanda Iftila'in Ya Shafa     Daga Mubarak Auwal Unguwa Uku.

 

Gwamnatin jihar Kano da buƙaci dukkan mutanen da suka ajiye muƙamansu domin yin takara a zaɓen Ƙananan Hukumomin dake tafe da suje a mayar musu da muƙaman su.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’amuran Cikin Gida Baba Halilu Ɗantiye ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sanarwar ta shafi waɗanda suke da sha’awar komawa kan muƙamin nasu a yanzu.

A cewar Ɗantiye “Bisa sahalewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ana sanar da ɗaukacin masu riƙe da muƙaman gwamnati da suka sauka daga kan mukaman nasu domin yin takara a zaben Kananan Hukumomi da ke ƙaratowa, amma hakan bata samu ba, kuma suke da sha’awar komawa kan mukamin nasu suje domin a mayar musu”.

A ƙarshe sanarwar ta buƙaci su je ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, wato Cabinet Office, daga ranar Talata, 24 ga watan Satumba, shekara ta 2024 domin cike takardun da suka kamata.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar