Daga Bello Usman.
Faɗuwar darajar Naira da kuma tsadar Man Fetur na ci-gaba da ruruta tashin farashin abubuwa a faɗin Najeriya.
Ana ɗan ganin sauƙi a tsadar kaya a ƙasar, duk da dai talakawa na ci-gaba ɗanɗana kuɗar su, koda ya ke akwai yiwuwar ‘yan Najeriya su daɗa samun sauƙi.
Faɗuwar darajar Naira, inda dala 1 kan kama daga naira 1,200 zuwa 1,600, da kuma tsadar mai na tauye wannan ɗan saukin da aka samu, tare da barazanar maido da tsadar rayuwar baya.
A hirarsa da wakilin Sashin Turanci na Muryar Amurka a Abuja, Gibson Emeka, wani injiniya mai ‘ya’ya hudu, mai suna Michael Anthony ya ce har yanzu ya na fama da tsadar kayan masarufi duk da ɗan sauƙin da aka samu, ko da ya ke tsadar ta ragu daga kashi 33.40% a watan Yuli zuwa kashi 32.15% a watan Agusta.
A cewar Injiniya Michael, “A watan Yuli, na sayi buhun shinkafa naira 65,000, amma a yanzu da na ke magana da kai, kwanaki uku da su ka gabata, na sai buhun shinkafa naira 95,000 a wannan kasar, kaga kenan har yanzu ina kashe kuɗi mai yawa wajen sayen kayan abinci a kasuwa a sakamakon hauhawar farashi saboda tashin mai”.
Ita ma, wata Blessing Ochuba, mai siyar da kayan abinci, a wata ‘yar maciya da ke wani gefen garin Abuja, ta ce “mutanen da ada kan sayi buhunan abinci, ayanzu rabi ma su ke saye, domin Ni kaina, ada, na kan yi sarin buhuna 10 na shinkafa, amma yanzu ba na iyawa.”
VOA Hausa.