Home / Flooding / Ambaliyar Borno: Gwamnatin Tarayya Zatai Aiki Da Ƙungiyoyi Wajen Tallafawa Al’ummar Maiduguri 

Ambaliyar Borno: Gwamnatin Tarayya Zatai Aiki Da Ƙungiyoyi Wajen Tallafawa Al’ummar Maiduguri 

Ambaliyar Borno: Gwamnatin Tarayya Zatai Aiki Da Ƙungiyoyi Wajen Tallafawa Al'ummar Maiduguri Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja. 

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙudiri Aniyar yin aiki da ƙungiyoyin Sa-kai, domin tallafawa al’ummar da Ambaliyar ruwa ta mamaye gidajensu, a Maidugurin Jihar Borno dake Arewa maso gabashin ƙasar.

Maitaimaki na Musamman ga mataimakin Shugaban ƙasa kan harkokin shari’a, Barista Bashir Maidugu ne ya sanar da hakan, a yayin da yake karɓar kayayyakin tallafi daga wasu ƙungiyoyin Sa-kai a Abuja fadar mulkin Najeriya.

Ƙungiyoyin da suka kai tallafin sun haɗar da Gidauniyar inganta rayuwar ‘Yan Najeriya tun daga matakin karkara (GBNI), da kuma Gidauniyar Fatomobu Dikwa.

Ambaliyar Borno: Gwamnatin Tarayya Zatai Aiki Da Ƙungiyoyi Wajen Tallafawa Al'ummar Maiduguri 

Barista Maidugu ya kuma yaba wa ƙungiyoyin dama Ɗaiɗaikun al’umma, a bisa abinda ya kira namijin ƙoƙarin da suka yi wajen miƙa sakon jaje da kuma tallafi ga al’ummar jihar Borno.

Adan haka ya ce gwamnatin Najeriya dama ta Jihar Borno zasu yi aiki da ƙungiyoyin Sa-kai hannu da hannu, domin tallafawa waɗanda wannan al’amari ya shafa.

A nata jawabin, Daraktar Hulɗa da jama’a da tsare-tsare ta Gidauniyar GBNI, Hajiya Rizkatu Abdul’aziz, ta bayyana cewa aikin su na ci-gaba da gudana a Birnin Maidugurin Jihar ta Borno, tun bayan afkuwar wannan iftila’in a ranar goma ga watan satumbar nan da muke ciki.

Haka kuma Rizkatu ta miƙa sakon godiya ga waɗanda suka tallafa musu har suka kai ga wannan nasarar, musamman shelkwatar tsaron Najeriya bisa jagorancin hafsan hafsohin tsaron kasar, Janar Christopher Gwabin Musa.

A ƙarshe ƙungiyoyin biyu sun ce sunan nan suna ci-gaba da kai kayan tallafi zuwa Jihar Borno, daga jihohin Kano, Kaduna, Plateau da Naija da kuma babban birnin tarayya Abuja.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar