Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja.
Tsohon Darakta a hukumar raya yankin Arewa maso gabashin Najeriya, Chief David Sabo Kentai, ya buƙaci masu hannu da shuni da su ƙara ƙaimi wajen taimakawa al’ummar da Ambaliyar ruwan ta shafa a Maidugurin jihar Borno.
Kentai yayi wannan kiran ne, a yayin da yake miƙa saƙon sa na jaje ga gwamnati da al’ummar jihar Borno, inda ya ce a halin yanzu suna matuƙar buƙatar tallafi domin farfaɗowa daga wannan Ambaliyar ruwa da yayi sanadiyar tafka asarar rayuka da ɗumbin dukiya.
Har Ila yau David, wanda ya kasance tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Taraba, yace wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar jihar Borno ke kukan targaɗe, sai kuma ga karaya ta samu.
Bugu da ƙari ya yabawa hukumar ta NEDC da sauran waɗanda suka bada tallafi, domin agazawa waɗanda iftila’in ya rutsa da su, inda yayi fatan ganin Mahukuntan yankin sun ɗauki matakan rigakafin faruwar hakan anan gaba.
Kawo yanzu dai Ɗaiɗaikun al’umma da ƙungiyoyin Sa-kai na ƙasa da ƙasa, gami da na gida Najeriya, haɗi da Majalisar ɗinkin duniya na ci-gaba da miƙa tallafin kuɗaɗe da kayan aiki dama abinci, ga gwamnati da al’ummar Jihar ta Borno, a sakamakon ambaliyar ruwan da ya faru ranar goma ga watan satumbar nan da muke ciki.