Daga Bashir Gasau.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi, ta sami nasarar kama wani Matashi, wanda take zargi da haƙe Ƙaburbura yana satar Rodi a wata maƙabartar mabiya addinin Kirista.
Kakakin rundunar na jihar Bauchi, SP Ahmed Muhammed Wakil ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya ce sun kama matashin me suna Dauda Saidu, mazaunin unguwar yelwa da tsakar dare yana tsaka da wannan aiki na rashin Imani.
A cewar Sanarwar Wakil “A ranar 20 ga watan Satumbar nan ne muka kama matashin me kimanin shekaru 21, ya shiga maƙabartar mabiya addinin Kirista dake unguwar Yelwan Kagadama ta jihar, inda yake haƙe Ƙaburbura yana cire Rodinan dake ciki da talatainin dare”.
Kuma tuni wanda ake zargin ya amsa laifin sa, harma ya ce ba wannan ne karon farko ba, domin kuwa yasha haƙa a baya kuma ya siyar da su akan farashin da ya kama daga Naira 9,500, 12,000 da kuma Naira 5,500.
Toh sai dai kuma ya ce ba komai yake yi da kuɗin ba, sai siyen kayan abinci da kuma Tabar wiwi domin yayi amfani dasu.
Adan haka rundunar ta ce zata gurfanar da shi a gaban Kotu da zargin Kutse, Barnata Duniya da kuma Sata, domin ya girbi abinda ya shuka.
A ƙarshe Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya shawarci iyaye da ma sauran al’umma su dinga sanya idanu akan yaran su, duba da matuƙar muhimmancin da hakan yake dashi.