Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja.
Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN), ta bayyana ƙwarin gwuiwar da take dashi akan rahoton kwamitin Farfesa Jega, na magance rikicin dake faruwa a tsakanin Makiyaya da kuma Manoma.
Shugaban ƙungiyar MACBAN na Najeriya, Baba Usman Ngelzarma ne ya bayyana hakan, a yayin zantawar sa da jaridar GTR Hausa a Abuja, inda ya ce ba’a taɓa samar da irin wannan kwamiti ba a tarihin ƙasar.
Ngelzarma ya ƙara da cewa, akwai alamun kwamitin da Farfesa Attahiru Jega ya jagoranta ya zaƙulo hanyoyin magance matsalar, duba da yadda ya ƙunshi Masana daga ɓangarori daban-daban.
A cewar Shugaban MACBAN na ƙasa, “Babu shakka idan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da rahoton kwamitin zai magance dukkan matsalolin, a sakamakon yadda ya ƙunshi hanyoyin da za’a ƙirƙiri hukumar, alkinta ayyukan ta dama samar da tsarin zaman lafiya a tsakanin ɓangarorin biyu”.
Haka kuma aiwatar da tsarin zai taka muhimmiyaar rawa wajen magance matsalar rikicin, duba da yadda Gwamnatin ta bawa ɓangaren muhimmanci a wannan lokaci.
Bugu da ƙari ya bayyana yadda tsarin zai haifar da inganta harkar kiwo dama tattallin arziƙin ƙasar, matuƙar aka samar da isashshen Kuɗi da kuma ƙwararrun Ma’aikata.
Adan haka ne yayi fatan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gaggawar aiwatar da rahoton kwamitin, domin amfanin fannin tattallin arziƙin ƙasar dama talakawa gaba-ɗaya.
A ƙarshe ya shawarci waɗanda lamarin ya shafa, su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace da zarar Gwamnatin tarayya ta aiwatar da shi.