Home / Flooding / Babu Barazanar Ambaliyar Ruwa A Madatsar Ruwan Challawa Goje – MD Hadejia Jama’are

Babu Barazanar Ambaliyar Ruwa A Madatsar Ruwan Challawa Goje – MD Hadejia Jama’are

Babu Barazanar Ambaliyar Ruwa A Madatsar Ruwan Challawa Goje - MD Hadejia Jama'are            Daga Bashir Gasau.

 

Hukumar raya Kogunan Hadejia da Jama’are ta Najeriya, ta bada tabbacin cewar babu wata barazanar faruwar ambaliyar ruwa a madatsar ruwa ta Challawa Goje (Gorge), dake ƙaramar Hukumar Ƙaraye ta jihar Kano.

Manajan Daraktan hukumar me kula da Jihohin Kano, Jigawa da kuma Bauchi, Alhaji Ma’amun Da’u Aliyu ne ya bada tabbacin a yayin ziyarar aikin da ya jagoranci manyan Jami’an hukumar zuwa Madatsar Ruwan, inda ya ce tuni ruwan ya fara janye wa.

Babu Barazanar Ambaliyar Ruwa A Madatsar Ruwan Challawa Goje - MD Hadejia Jama'are

A cewar Manajan Daraktan hukumar wadda take ƙarƙashin ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayyar Najeriya “A makon da ya wuce munje da ku Madatsar ruwa ta Tiga, inda a yau kuma kamar yadda kuka gani da idon ku munzo wannan ƙaramar Madatsar ruwa ta Challawa Goje (Gorge), kuma ita tana cikin ƙoshin lafiya kamar yadda Tiga take”.

Bugu da ƙari ya ce wannan ƙaramar Madatsar ruwa wadda take ɗaukar ruwa me yawan Lita Bilyan 930, ana amfani da ita wajen yin noman rani a yankin Hadejia dake jihar Jigawa, a inda ruwan yake dangana wa da babban Kogin Ƙasar Chadi.

Babu Barazanar Ambaliyar Ruwa A Madatsar Ruwan Challawa Goje - MD Hadejia Jama'are

Haka kuma Alhaji Ma’amun ya ce Madatsar Ruwan me girman Kilomita 100 (square) da kuma zurfin Mita 40, tana tara ruwan ne bayan ya taho daga Arewacin jihar Kaduna da kuma wasu sassan jihar Katsina.

Adan haka ya buƙaci al’ummar dake maƙwabtaka da yankin dama sauran sassan ciki da wajen jihar Kano su kwantar da hankalin su, su ci-gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.

Babu Barazanar Ambaliyar Ruwa A Madatsar Ruwan Challawa Goje - MD Hadejia Jama'are

A hannu guda ya jaddada ƙoƙarin da suke yi wajen magance wa al’ummar Masarautar Ƙaraye matsalar su na rashin samun ruwan da zasu dinga noman rani, inda ya ce suna nan suna aiwatar da wannan aiki domin amfanin al’ummar yankin.

A ƙarshe ya shawarci masu Gonakin dake kusa da Madatsar suyi gaggawar ɗebe amfanin gonar su da zarar ya ƙosa, domin gudun shigar ruwa cikin gonakin su idan ya sauka daga kan hanyar sa.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar