Home / Labarai / Hadari: Sarkin Kano Na 15 Ya Jajantawa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya

Hadari: Sarkin Kano Na 15 Ya Jajantawa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya

Haɗɗari: Sarkin Kano Na 15 Ya Jajantawa Rundunar 'Yan Sandan Najeriya           Daga Bello Usman.

 

 

 

Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana rasuwar jami’an ‘yan sanda biyar da kuma jikkatar wasu 11, a matsayin wata babbar Jarrabawa ga rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Sarkin ya bayyana hakan ne ta cikin saƙon jaje da babban Sakataren yaɗa Labaran sa, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya ce lamarin abin tausayi ne da kuma ban tsoro.

A cewar Sarki na 15, “Rasuwar jami’an ‘yan sanda a bakin aikinsu wani babban lamari ne mai ban tausayi da ban tsoro, duba da irin gagarumar rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma a matakin ƙasa baki ɗaya”.

Ya kuma ce ayyukan da suke yi na cike da sadaukarwa ga al’umma, wanda ya baiwa ‘yan ƙasa damar gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.

Daga nan sai ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga babban sufeto na rundunar ‘yan sandan Najeriya, da Mataimakinsa mai kula da shiyya ta ɗaya dake Kano dama Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, harma da iyalai da ‘yan uwan ​waɗanda iftila’in ya shafa.

Bugu da ƙari ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu yasa sun huta, su kuma waɗanda suka jikkata ya basu lafiya cikin gaggawa, ya kuma kiyaye faruwar hakan a nan gaba.

A ƙarshe ya shawarci Direbobi da masu amfani da ababen hawa, su riƙa kiyaye ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa, musamman a kan manyan hanyoyi domin ci-gaba da ceto rayukan ‘yan kasar dama kiyaye faduwar haɗɗura.

Da Asubahin jiya Talata ne, haɗarin ya faru a garin Ƙarfi dake kan hanyar Kano zuwa Zaria, inda Mutum 5 suka rasu, yayin da 11 suka jikkata.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar