Home / Business / Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Sabuwar Yarjejeniyar Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Sabuwar Yarjejeniyar Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Sabuwar Yarjejeniyar Inganta Tsarin Shugabancin Duniya               Daga Bashir Gasau.

 

Majalisar Ɗinkin Duniya, ta amince da sabuwar yarjejeniyar inganta tsarin shugabancin duniya.

Sakatare Janar na Majalisar, Antonio Gutterres ne ya bayyana hakan, a yayin jawabin buɗe taron Shugabannin duniya a ranar 22 ga watan Satumbar Shekarar 2024, inda ya ce an tabbatar da yarjejeniyar ne saboda gaba.

A cewar Gutterres “Mun cimma yarjejeniyar ƙasa da ƙasa mafi fa’ida a cikin shekaru da yawa wacce ta shafi sabbin fannoni, da nufin samar da dukkan abubuwan da zasu tabbatar da cewa cibiyoyin ƙasa da ƙasa za su iya ba da gudunmawa ta fuskar canza duniya, domin matuƙar ba muyi hakan ba, toh ba zamu iya samar da abinda zai dace da jikokinmu na gaba ba”.

Ya kuma ƙara da cewa, Shugabanni sun tsara hangen nesa na tsarin ƙasa da ƙasa wanda zai iya cika alƙawuransu na wakilci a duniya, na jawo makamashi da ƙwarewar gwamnatoci, ƙungiyoyin jama’a da kuma sauran manyan abokan hulɗa.

Sakatare Janar ɗin ya kuma lura cewa yarjejeniyar zata dasa harsashi domin ɗorewar zaman lafiya da adalci, ci-gaba mai ɗorewa, sauyin yanayi, hadin gwiwa kan abin da ya shafi fasahar zamani (Digital), haƙƙin ɗan adam, inganta rayuwar matasa da al’ummomi masu zuwa, da kuma sauya tsarin mulkin duniya.

Abubuwan da yarjejeniyar fannin zaman lafiya da tsaro ya ƙunsa sun haɗar da wani gagarumin yunƙuri na kawo sauye-sauye a kwamitin sulhun domin inganta ingancinsa da wakilcinsa, musamman magance rashin wakilci na tarihi a Afirka.

Bugu da ƙari, akwai wani sabon alƙawari na ɓangarori da yawa na kawar da makaman nukiliya, da nufin kawar da shi baki ɗaya.

Akwai kuma yarjejeniyar ƙarfafa tsarin ƙasa da ƙasa wanda ke kula da sararin samaniya tare da maida hankali kan hana tseren makamai a sararin samaniyar, domin tabbatar da samun daidaiton damar samun fa’idar binciken sararin samaniya.

Sai yarjejeniya ta ƙarshe ita ce ɗaukar matakan hana amfani da makamai da kuma amfani da sabbin fasahohi, kamar muggan makamai, tare da tabbatar da aiwatar da dokokin yaƙi ga waɗannan fasahohin.

A fannonin ci-gaba me ɗorewa da kuma yanayi kuwa, abubuwan da yarjejeniyar ta cimma sune, yarjejeniya mafi girma da aka taɓa samu a Majalisar Dinkin Duniya game da sake fasalin tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa, don samar da wakilci da hidima ga ƙasashe masu tasowa.

Wannan Yarjejeniya ta ƙunshi bawa ƙasashe masu tasowa babbar dama wajen yanke shawara a cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa, da ƙara samar da kuɗaɗe daga bankunan raya ƙasa domin tallafawa buƙatun su na ci-gaba, baya ga yin nazari kan gine-ginen basussuka, don tabbatar da ci-gaban rance don zuba jari a nan gaba.

Yarjejeniyar ta biyu ita ce maida hankali kan ƙarfafa tsarin kiyaye hada-hadar kuɗi na duniya domin kare masu rauni a lokutan matsalolin kuɗi da tattalin arziki, harma da tunkarar ƙalubalen sauyin yanayi ta hanyar samar da ƙarin kuɗaɗe don taimaka wa ƙasashe su zuba jari a fannin makamashin da aka sabunta.

Sai ta Uku, jaddada muhimmancin auna ci-gaban ɗan Adam fiye da GDP, ta hanyar la’akari da jin daɗin sa dama na duniya gaba-ɗaya, dama alƙawarin ƙaddamar da mafi ƙarancin matakin haraji na duniya.

Sai Yarjejeniya ta ƙarshe, ta tabbatar da wajibcin ƙayyadaddun yanayin zafi a duniya zuwa kashi 1.5 a ma’aunin salshiyos, sama da matakan masana’antu da kuma sauye-sauye daga ɓurɓushin mai a cikin tsarin makamashi don cimma iskar sifili ta 2050.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar