Home / Government / UNGA 79: Muna Neman A Yafewa Najeriya Bashin Da Ake Binta – Tinubu 

UNGA 79: Muna Neman A Yafewa Najeriya Bashin Da Ake Binta – Tinubu 

UNGA 79: Muna Neman A Yafewa Najeriya Bashin Da Ake Binta - Tinubu              Daga Bello Usman.

 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci a yafe wa Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa bashin da ake binsu.

Tinubu yayi wannan kira ne a yayin da yake yiwa Shugabannin duniya jawabi, a wurin babban taron majalisar ɗinkin duniya karo na 79, wanda ya gudana Shelkwatar Majalisar dake birnin New York, na ƙasar Amurka.

Tinubu, wanda ya sami wakilcin Mataimakinsa Sanata Kashim Shettima ya ƙara da cewa, hakan nada matuƙar muhimmanci ga ƙasashe masu tasowa musamman Najeriya.

Sanarwar da Kakakin Mataimakin Shugaban ƙasar Mr Stanley Nkwocha, ya fitar a Yau Laraba ta ce yafe bashi zai magance matsaloli masu yawa da ƙasashe masu tasowa suke fuskanta.

Haka kuma ya bayyana hakan a matsayin ƙwarin gwuiwar da ƙasashen suke da shi domin kare harkar cinikayyar su daga rushe wa.

A ƙarshe ya bada tabbacin cewa, hakan shine zai magance matsalar rashin ƙwarin gwuiwar da masu zuba jari suke dashi, na shiga irin waɗancan ƙasashe.

NAN.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar