Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja.
Hukumar dake kula da ilimin Almajirai da Yara da basa zuwa Makaranta ta Najeriya wato NCAOOSCE atakaice, ta kaddamar da kwamiti da zai hada kan kungiyoyin makarantun allo na kasa domin samar da kungiya daya wadda za ta rika mu’amala da ita a madadin dukkanin kingiyoyin.
Shugaban hukumar ta NCAOOSCE Dakta Muhammad Sani Idiris ne ya kaddamar da kwamitin a shelkwatar hukumar dake Abuja fadar mulkin Najeriya.
Dakta Muhammad Sani Idris ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin a Shelkwatar hukumar dake Babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce an basu makonni uku domin su miƙa rahoton su.
Kwamitin Mai Mutum takwas zai yi aiki ne wajen zaƙulo ƙungiyoyin Almajirai dake sassan Najeriya, domin a samar da kungiya Daya tilo da zata jagoranci yin mu’amula da hukumar ta NCAOOSCE maimakon kungiyoyi sama da dubu biyu dake fafutukar kare hakkin Almajirai.
A cewar Dakta Muhammad Sani Idris “Mun ƙaddamar da kwamiti ne domin tattara alkaluman ƙungiyoyin Almajiran dake faɗin Najeriya, ta yadda za’a haɗe su a inuwa guda wato magana da Murya daya domin samun sauƙin aiwatar da shirin Gwamnatin tarayya na inganta fannin”.
Tun da fari dai Shugaban hukumar ta NCAOOSCE Dr Muhammad Sani Idiris ya bayyana cewa nan da Yan makonni masu zuwa zasu ninkaya kudancin Najeriya domin zama da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a yankin domin lalubo bakin zaren kawo karshen Yara da basa zuwa Makaranta da aka kiyasata sun Kai miliyan Ashirin, yayin da kididdiga suka Nuna cewa akwai Almajirai akalla miliyan talatin a fadin Najeriya.
A nasa ɓangaren Shugaban kwamitin da aka kafa Sayyadi Ƙassim Yahaya Wanda har Ila yau ke kasancewa Shugaban kungiyar Jamiyytul Ansarudden Attajaniyya ta kasa, ya bayyana aikin a matsayin me sauƙi, duba da yadda aka zaƙulo waɗanda suke da ilimi a fannin harma ya ce da alamun kwalliya zata biya kuɗin Sabulu.
A ƙarshe ya bada tabbacin cewar kwamitin nasu zai yi dukkan mai yiwuwa wajen sauke nauyi da aka ɗora musu, domin amfanin masu harkar karatun Allon dake lungu da saƙo na Najeriya.