Daga Ɗantala Uba Kura.
Aƙalla yara huɗu ne suka tsallake rijiya da baya, a sakamakon yadda wata rijiya ta rufta da su, lamarin da ya yi sanadiyyar karyewar ɗayan su a ƙwauri, a yayin da sauran Ukun suka jikkata.
Lamarin ya faru ne a Unguwar Tafasa dake ƙaramar hukumar, inda tsohowar Rijiyar wadda ta shafe sama da shekaru ɗari biyu ta rufta da yaran a dai-dai lokacin da suka zo wuce wa ta wurin.
Al’ummar dake maƙwabtaka da Rijiyar sun tabbatar da cewa, dama ta jima tana yi wa gidajen su barazana dama su kansu, a sakamakon ƙaton Kogon dake cikin ta.
Tuni Daraktan Mulkin ƙaramar hukumar ta Kura Alhaji Sabo Muhammad, ya yi alkawarin cike wata Rijiya bisa sahalehar Gwamnatin Jihar Kano.
A ƙarshe sun yi fatan mahukuntan zasu yi gaggawar cike musu Rijiyar, domin fitar da su daga cikin wannan barazana da suke fuskanta a tsawon waɗannan shekaru.