Daga Bashir Gasau.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Hassan Muhammad (Jarman Gusau), ya buƙaci Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Dauda Lawal, da ya maida hankali wajen cika alƙawuran da ya yi wa Talakawan jihar, maimakon yawo da hankalin su.
Jarman Gusau na wannan bayani ne, a sakamakon yadda ya ce “Gwamnan ya bar Jaki yana dukan Taiki”.
Tsohon Mataimakin Gwamnan ya ƙara da cewa, Gwamnan Jihar Zamfara ya yi alƙawarin samar da tsaro a lokacin yaƙin neman zaɓen sa, amma kuma yanzu sai ya maida hankali wajen zargin tsohowar Gwamnatin da ta gabata na akan cewa tana da hannu akan matsalar tsaron jihar, duk da cewar tsohon Gwamnan shine ƙaramin Ministan tsaron Najeriya a halin yanzu.
Haka kuma kowa ya san a lokacin Gwamnatin Matawalle munyi bakin ƙoƙarinmu wajen magance matsalar tsaron jihar, ta hanyar ceto mutane masu yawa da ‘yan fashin Daji suka sace, mun ƙwato ɗaruruwan Shanu cikin shekara guda, baya ga samar wa Jami’an tsaro Motoci da Babura sama da ɗari hudu domin yaƙar ‘yan Ta’addan.
Wannan kaɗai ya isa ya nuna irin ƙoƙarin da Gwamnatinmu tayi, na ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar tsaron saboda muhimmancin da yake dashi.
“Saboda haka danganta Gwamnatinmu da alaƙa da Ta’addanci kamar wani salo na kauda hankalin mutanen jihar Zamfara, daga alƙawuran da Gwamna Dauda Lawal yayi musu na magance matsalar tsaron dama sauran matsalolin dake damun su”.
Adan haka tsohon Mataimakin Gwamnan ya shawarci Gwamna Dauda Lawal ya maida hankali wajen ƙoƙarin magance matsalolin dake damun jihar, maimakon ƙoƙarin shafa wa Gwamnatin baya kashin Kaji dama ɓata sunan ƙaramin Ministan tsaron Najeriya ba.
A ƙarshe ya yi fatan Gwamnan zai sanya buƙatun al’ummar jihar sama da Milyan 4 a gaba, domin ciyar da su gaba a dukkan fannonin da zai shafi rayuwar su ta yau da kullum.