Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja.
Da yammacin jiya laraba aka sake rantsar da Honarabul Yusuf Adamu, a matsayin kwamishinan hukumar sauraron koken al’umma ta kasa, wato public complain commission (PCC).
Yusuf Adamu, ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin kwamishinan hukumar dake wakiltan jihar Borno, a karo na biyu.
Harma ya bada tabbacin yin amfani da gogewar sa wajen ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, dangane da nauyin da ya rataya a wuyansa.
Kafin zaman sa Kwamishina a hukumar, Honarabul Yusif Adamu ya kasance mai bawa Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima shawara a fannin Siyasa, lokacin da yana Gwamnan Jihar su ta Borno.
Duk da cewa an takaita mahalarta bikin rantsuwar, wanda ya gudana a Majalisar dokokin Najeriya, kaɗan daga cikin ‘yan Uwa da abokanin arziƙi ne suka samu damar halartar Ƙwarya-ƙwaryar bikin.