Home / Business / Saudiyya Da Kano: Muna Da Alaƙa Ta Sama Da Shekaru 100 – Gwamnan Kano

Saudiyya Da Kano: Muna Da Alaƙa Ta Sama Da Shekaru 100 – Gwamnan Kano

Saudiyya Da Kano: Muna Da Alaƙa Ta Sama Da Shekaru 100 - Gwamnan Kano         Daga Murtala A. Baba.

 

Daɗaɗɗiyar alaƙar samar da Shekaru 100, dake tsakanin ƙasar Saudiyya da kuma jihar Kano ta ƙara fito wa fili, a yayin da ƙasar Saudiyyan ke ci-gaba da bikin shekaru 94 da samar da Tuta.

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan ta cikin saƙon taya ƙasar Saudiyya murnar ganin waɗannan shekaru, wanda ya miƙa ta hannun Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a yayin wani babban taro da aka gudanar a ofishin Jakadancin Saudiyya dake jihar.

Da yake jawabi a wurin taron, Mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Gwarzo, ya bayyana ɗabi’u da kuma Al’adu dama koyarwar Addinin Musulunchi a tsakanin al’ummar ɓangarorin biyu, na a matsayin dalilin da ya sanya alaƙar ta yi wannan dogon zango harma ake ci-gaba da mutunta juna dama danƙon zumunci.

Ofishin Jakadancin ƙasar Saudiyya a jihar Kano ne suka shirya wannan babban taro ƙarƙashin jagorancin babban Jami’in dake kula da ofishin Khalil Ahmad Adamawi, domin bin sahun al’ummar ƙasar tasu me albarka.

Harma da yake jawabi Khalil Adamawi, ya ce abin tarihin da Sarki Abdulaziz bin Abdulrahman Al Saud ya samar a shekarar 1932, shine ya ƙara ƙwarin gwuiwar Samar da mulkin adalci a ƙasar tasu.

A cewar Ahmad Adamawi, “Alaƙa a tsakanin Saudiyya da Najeriya, musamman jihar Kano na da dogon tarihin, inda ya ƙara tabbatar da abota da zumuncin dake tsakanin ɓangarorin biyu.

Taron dai ya sami halartar manyan muƙarraban Gwamnati, Shugabannin harkokin Diflomasiyya, wakilan ƙungiyoyin duniya, fitattun ‘yan Kasuwa dama wakilai daga Jihohin Kaduna da kuma Zamfara.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar