Home / Business / ‘Yan Sandan Bauchi Sun Kama Barawon Ƙarfen Digar Jirgin Ƙasa

‘Yan Sandan Bauchi Sun Kama Barawon Ƙarfen Digar Jirgin Ƙasa

'Yan Sandan Bauchi Sun Kama Barawon Ƙarfen Digar Jirgin Ƙasa             Daga Bashir Gasau.

 

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi, ta sami nasarar kama wani Matashi da take zargi da satar ƙarfen Digar Jirgin Ƙasa guda 95.

Kakakin rundunar na jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya ce tuni aka gano ƙarafunan gaba-ɗaya.

Rundunar ta kama matashin me suna Heli Hassan ɗan kimanin shekaru 29, bayan wani sahihin rahoto da ƙungiyar masu kayan Gwan-gwan ta basu.

Toh sai dai tuni wanda ake zargin ya amsa laifin sa, inda ya ce sun haɗa kai da wani Mutum me suna Jacob Sulaiman wanda ya gudu, suka sace ƙarafunan bayan sun kwance su a unguwar Inkil dake jihar ta Bauchi.

Wannan ɗanyen aiki nasu dai ya taɓa harkokin yau da kullum na al’ummar yankin, ta hanyar kassara tattallin arziƙin su, dama haifar da matsala a wannan Gadar Jirgin Ƙasa ta Inkil wadda ta dangana da jihar Gombe.

Haka kuma sanarwar ta ce rundunar tana nan tana gudanar da zuzzurfan bincike, baya ga baza komar neman Jacob Sulaiman wanda Zakara ya bashi Sa’a.

Bugu da ƙari rundunar ta bayyana wannan nasara a matsayin wata alama, dake ƙara nuna jajircewar ta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A ƙarshe Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya buƙaci al’umma da su ƙara sanya idanu ta hanyar kula da duk wani motsi da basu gamsu dashi b, ta yadda zasu dinga bada rahoton gaggawa akan wannan lambar “081 51 84 94 17” domin ɗaukar matakin da ya dace.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar