Home / Labarai / Kano: Ana Zargin Wasu Matasa Da Kashe Abokinsu Bayan Ɗauko Shi Daga Gida

Kano: Ana Zargin Wasu Matasa Da Kashe Abokinsu Bayan Ɗauko Shi Daga Gida

Kano: Ana Zargin Wasu Matasa Da Kashe Abokinsu Bayan Ɗauko Shi Daga Gida           Daga Bello Usman.

 

 

A daren jiya ne dubun wasu Matasa ta cika, a sakamakon yadda aka zarge su da kashe Abokin su bayan sunje har gida sun ɗauko shi.

An dai kama Matasan ne a ƙauyen ‘Yar Kanya dake ƙaramar hukumar Bichi, a dai-dai lokacin da ake zargin suna ƙoƙarin jefar da gawar abokin nasu.

Wasu ganau da suka tabbatar wa da jaridar GTR Hausa faruwar lamarin sunce, wani magidanci ne ya fara ankara da lamarin, bayan sun ɗauko gawar matashin a cikin Baburin Adaidaita Sahu suna ƙoƙarin yarda ita bayan sun sallami me Baburin ya tafi abinsa.

Toh sai koda yayi ƙoƙarin tona musu asiri sai suka yi ƙoƙarin illata shi, kafin daga bisani mutanen dake kusa da wurin suka ankara da abinda ke faruwa.

Kuma bayan sun damƙe Matasan suka iske su ɗauke da Wuƙa, Tsitaka, Sirinji guda Ɗari da kuma Ƙwaya samfurin Roti, mafari kenan da suka damƙa su a hannun Jami’an tsaro.

Kuma bayan damƙa su a hannun ‘yan Sandan Bichi domin su bincika lamarin ne, majiyar da ta tsegunta mana wannan labari ta shaida mana cewar iyayen yaron da aka kashe, sun tabbatar da cewar waɗanda ake zargin ne suka zo har gida suka tafi dashi.

Akan wannan batu Jaridar GTR Hausa ta tuntuɓi Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya ce zai bincika lamarin harma yayi alƙawarin waiwayar mu da zarar ya tattara bayanai.

Toh amma ku ci-gaba da bibiyar mu domin jin matsayar rundunar ‘Yan Sandan Kano akan lamarin, dama dalilin waɗanda ake zargin na kisan Abokin nasu idan sun magantu.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar