Daga Musa Aminu Iyah.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, ya buƙaci ‘yan Jarida da su yi amfani da ƙwarewar su, wajen wayar da kan al’umma akan muhimmancin zaman lafiya a Najeriya.
Jami’in Diflomasiyyar Ofishin a Najeriya, Mr. Brian Neubert ne ya buƙaci hakan, a yayin taron bita na yini biyu, da ofishin su haɗi da Gidauniyar Dhul jalalu wato (Dhul jalalu Chatitable foundation), suka shiryawa Ma’aikatan Radio da Talabijin a Abuja fadar mulkin Najeriya.
Taron wanda Ma’aikatan Radio na Abuja da Kuma wasu daga Kaduna dake Arewacin Najeriya suka halarta ya maida hankali ne, wajen yin bita akan ayyukan radio kamar haɗa rahoto, rubuta labarai da karantawa da kuma gano ingancin labari, haɗi da amfani da sabuwar fasahar AI a aikin Radio.
Mr Neubert ya bayyana irin babbar rawar da ‘yan Jarida suke takawa a cikin al’umma, harma ya basu tabbacin cewar Ofishin Jakadancin Amurka dake Najeriya zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun sami ‘yancin gudanar da aikinsu ba tare da tsoro ko barazana ba.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka jagoranci bada bitar, Hajiya Binta Abubakar Mora, ta hori mahalarta taron da su dinga amfani da kalmomi masu sauƙi a yayin da suke isar da saƙo ga al’umma.
Shima wani Ƙwararre a fannin aikin yaɗa labarai dake ofishin Jakadancin, Mr. Joseph Adah, wanda ya yi lakca akan amfani da sabuwar fasahar AI da kuma sabbin kafafen zamanin da ake amfani da su wajen isar da saƙo ga al’umma, ya buƙaci ‘yan Jarida su dinga amfani da su wajen isar da saƙon da zai amfani al’umma.
Da take gabatar da jawabin bankwana, jagorar gabatar da Taron bitar, wacce har Ila yau ke kasancewa jami’ar ofishin Jakadancin Amurka, Hajiya Aisha Sulu Gambari, ta buƙaci waɗanda suka sami wannan tagomashi da su kasance sun ƙulla alaƙa domin taimakekeniya a tsakaninsu, musamman akan abinda ya shafi aikin da suka sanya a gaba.
Haka kuma ta bada tabbacin cewa a shirye ofishinsu yake ya tsayawa duk wani Ɗan jarida da akaci zarafinsa, amma ta shawarci manema labarai da su guji yiwa dokokin ƙasa hawan ƙawara a sa’ilin da suke bakin aiki.
Suma mahalarta taron sun bayyana godiyarsu ga Gidauniyar Dhul jalalu wato (Dhul jalalu Chatitable foundation), dama Ofishin Jakadancin Amurka a bisa ɗaukar nauyin wannan bita, harma suka yi alƙawarin yaɗa abinda suka koya ga sauran abokan aikin da suke tare dasu a tashoshi daban-daban.