Home / Government / Muna Fatan Mahukunta Zasu Kawo Ƙarshen Kai Marasa Laifi Gidan Gyaran Hali – UDHR

Muna Fatan Mahukunta Zasu Kawo Ƙarshen Kai Marasa Laifi Gidan Gyaran Hali – UDHR

Muna Fatan Mahukunta Zasu Kawo Ƙarshen Kai Marasa Laifi Gidan Gyaran Hali - UDHR         Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Declaration of Human Right (UDHR), dake jihar Kano a Arewacin Najeriya, ta buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su kawo ƙarshen matsalar kai Marasa laifi gidajen gyaran halin dake faɗin ƙasar nan.

Babban Daraktan ƙungiyar, Kwamared Umar Sani Galadanci ne ya buƙaci hakan, ta cikin wani saƙon murya da ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya ce babu shakka ana tsare mutane masu yawa ba tare da sun aikata laifin komai ba.

A cewar Galadanci, “Binciken mu ya gano yadda sama da kashi 75 na mazauna gidajen gyaran halin Kurmawa da Gwauron Dutse, suka shafe tsawon lokaci suna jiran shari’a, wanda kuma ƙunshin tuhumar da aka sanya musu ba ita suka aikata ba”.

Ya kuma ƙara da cewa, wannan matsala ta samo asali ne daga irin binciken da Jami’an ‘yan sanda suke gudanarwa da kuma irin jan ƙafar da Shari’u suke yi a Kotunan Jihar.

Adan haka ƙungiyar ta buƙaci dukkan ɓangarorin su ɗauki matakan da suka kamata, domin magance wannan matsala ta yadda za’a daina kai mutanen da basu ji ba kuma basu gani ba.

A hannu guda ƙungiyar ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, a bisa jin kiran su da yayi na samar da kwamitin da zai bibiyi halinda al’ummar jihar Kano suke ciki a Kamfanoni masu zaman kansu.

Harma ta yi fatan kwamitin zaiyi aikin sa tsakani da Allah, domin samar wa jihar Kano mafita akan tarin matsalolin da suke fuskanta a irin waɗannan Kamfanoni.

A ƙarshe ƙungiyar tayi fatan mahukuntan zasu ci-gaba da sanya buƙatun al’umma a gaba, maimakon tsarikan da su kaɗai zasu dinga amfana.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar