Home / Education / Operation Kauda Baɗala: Kwamishinan Hisba Na Bauchi Ya Ziyarci Daurawa A Kano

Operation Kauda Baɗala: Kwamishinan Hisba Na Bauchi Ya Ziyarci Daurawa A Kano

Operation Kauda Baɗala: Kwamishinan Hisba Na Bauchi Ya Ziyarci Daurawa A Kano            Daga Bashir Gasau.

 

A ƙoƙarin da take yi na kakkaɓe ayyukan alfasha a faɗin jihar Bauchi, hukumar Hisba ta jihar ta ziyarci Shugaban Hukumar Hisba na Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Kwamishinan Hukumar na jihar Bauchi, Barista Aminu Balarabe Isah ne ya jagoranci tawagar, zuwa Shelkwatar hukumar dake unguwar Sharaɗa dake birnin Kano.

Da yake ƙarin haske akan maƙasudin zuwan nasu, Barista Aminu ya ce sun zo ne domin su tattauna akan dabarun inganta aikin hukumar a jihar Bauchi, ta yadda za’a kauda ɗabi’u marasa kyau kamar Zinace-zinace, Shaye-shaye, da dangogin su.

Operation Kauda Baɗala: Kwamishinan Hisba Na Bauchi Ya Ziyarci Daurawa A Kano

Haka kuma ya yaba wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkhadir Mohammed (Khadimul Qur’an), a bisa cikakken goyon bayan da yake bawa hukumar, domin samun nasarar aikin da ta sanya a gaba na tsaftace jihar gaba-ɗaya.

Da yake maida jawabi, babban Kwamandan Hisba na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya godewa Allah da ya nuna masa wannan lokaci inda yayi maraba da tawagar, harma ya yaba wa Gwamnan Jihar Bauchi a bisa yadda yake bawa harkokin Addini muhimmanci, musamman hukumar Hisba wadda ke ƙoƙarin kawar da ayyukan Baɗala a faɗin jihar.

A cewar Daurawa, “Aikin Hisba aiki ne na tsoron Allah da tsarkake Zuciya, adan haka yana buƙatar goyon bayan Shugabanni, Malamai da sauran al’umma domin ta hakan ne za’a sami damar kawar da ayyukan Baɗala a fadin jihar”.

Haka kuma ya bayyana haɗin gwuiwa da ƙungiyar Kiristoci ta jihar (CAN), a matsayin abinda zai sanya aikin ya sami nasara da kuma kwanciyar hankali.

A ƙarshe Kwamishinan Hukumar Hisba na jihar Bauchi, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin jihar dama dukkan wasu masu ruwa da tsaki zasu basu cikakken haɗin kai da goyon baya, domin ƙudirin Gwamnatin jihar na kawo kyakykyawan canji a Jihar.

Sanarwar da Mashawacin Gwamnan Bauchi akan Kafafen Sada Zumunta, Alhaji Nuru Abdullahi (Baban Zarah) ya aiko wa jaridar GTR Hausa ta ce tawagar Hukumar ta ƙunshi ‘Yan Majalisar jihar guda Uku, waɗanda suka haɗar da me wakiltar Ƙananan Hukumomin Giade, Zungur da Galambi, dana ƙaramar hukumar Miri dama na ƙaramar hukumar Kirfi.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar