Daga Bashir Gasau.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi, ta tabbatar da kama wasu Ɗaliban Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBU) dake jihar , bisa zargin su da haɗa kai, haura gida da kuma Sata.
Kakakin rundunar SP Ahmed Muhammed Wakil ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa a yammacin yau Jumu’a.
Inda ya ce Ɗaliban Biyu ‘yan Aji 4 da kuma 5 a Jami’ar sun shiga wani gida ne, inda ake zargin sun saci kaya waɗanda suka haɗar da Talabijin ɗin Bango, Dikoda, babbar abar Sauti , ƙaramar Sifika, Takalmi, Bargon da kuma Sallaya.
Toh sai dai tuni waɗanda ake zargin suka amsa laifin su, harma suka ce ba komai ne ya kaisu wannan hali ba sai domin neman kuɗin yin Furojet ɗin shekarar su ta ƙarshe a Jami’ar.
A ƙarshe rundunar ‘Yan Sandan jihar, ƙarƙashin jagorancin CP Auwal Musa Muhammad, ta yi alƙawarin gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
A ƙarshe sanarwar ta buƙaci al’umma su ci-gaba da bada rahoton duk wani abu da basu gamsu dashi ba, domin ɗaukar matakin da ya kamata kuma akan lokaci.