Daga Bashir Gasau.
Ranar Talata me zuwa ita ce ranar 1 ga watan Oktoba, wanda kuma a ranar ne Najeriya zata cika Shekara 64 da samun ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya.
Adan haka ne Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara shirye-shiryen zuwa ranar, harma ta ayyana wasu abubuwa 3 dangane da zuwan ranar 1 ga Oktoban.
Abu na farko shine yadda a jiya Jumu’a Shugaba Tinubu ya jagoranci taron yiwa ƙasar addu’a, bayan kammala Sallar Juma’a a babban Masallacin Juma’a na ƙasa dake Abuja.
Taron Addu’ar ya sami halartar Kakakin majalisar wakilai Tajuddin Abbas, tsohon shugaban ƙasa na mulkin Soja Janar Abdussalami Abubakar da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo da sauran manyan ƙasar.
Haka kuma a daren jiya Shugaba Tinubu ya sake bada umarnin yin ƙaramin bikin ‘yancin kai, saboda yanayin da ƙasar ke ciki.
Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ne ya sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce gwamnatinsu na sane da halin matsi da ‘yan ƙasa ke ciki.
Sai abu na Uku shine Ayyana ranar Talatar a matsayin ranar hutu ga ‘yan ƙasar.
A inda wannan sanarwa ta fito ta cikin wata sanarwa da Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar a yau Asabar, dukka dai albarkacin ranar samun ‘yancin kan Najeriya.