Home / Flooding / Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Aikin Tsaftar Muhalli A Ƙananan Hukumomin Jihar 

Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Aikin Tsaftar Muhalli A Ƙananan Hukumomin Jihar 

Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Aikin Tsaftar Muhalli A Ƙananan Hukumomin Jihar               Daga Bashir Gasau.

 

Kwamishinan Ma’aikatar Gidaje da Muhalli na jihar Bauchi, Rt. Honarabul Ɗanlami Ahmed Kawule (Barden Arewan Bauchi), ya ƙaddamar da aikin tsaftar Muhalli a ƙananan Hukumomin Jihar Ashirin.

Barden Arewan Bauchi ya ƙaddamar da aikin ne a Unguwar Kobi, bisa cikakken goyon bayan Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, domin tabbatar da tsafta da Lafiyar al’ummar jihar.

Manufar ƙaddamar da aikin shine, tabbatar da tsafta a lungu da saƙo na jihar, Samarwa Matasa hanyar dogaro da kansu, ƙara samar da ayyukan ci-gaba, ciki harda gyaran Masallacin Unguwar Kobi, harma da gyara magudanan ruwa domin yin kandagarkin faruwar ambaliyar ruwa.

Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaddamar Da Aikin Tsaftar Muhalli A Ƙananan Hukumomin Jihar 

A cewar Kwamishinan, “Duba da yadda Gwamnan Bala Muhammad ya bawa tsaftar Muhallin al’umma muhimmanci, shiyasa muka himmatu wajen gudanar da irin wannan aiki akai-akai, domin ganin cewa al’umma suna yi kamar yadda aka tsara”.

Harma ya ce manufar shirin shine, tabbatar da tsaftar Muhalli, ƙarfafawa al’umma gwuiwar tsafta ce yankunan su, samarwa Matasa guraben aiki, samar da ƙarin ayyukan ci-gaba dama yin kandagarkin faruwar ambaliyar ruwa.

A ƙarshe sanarwar da Mashawacin Gwamnan akan kafafen sada zumunta, Alhaji Nuru Abdullahi (Baban Zahra), ya aiko wa jaridar GTR Hausa ta ce, Gwamnatin jihar zata ci-gaba ƙoƙari wajen inganta lafiya da samar da kyakykyawan Muhalli ga talakawan jihar.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar