Home / Government / Mun Shirya Yafewa Masu Yaɗa Bidiyon Batsa A Kafafen Sada Zumunta – Hisba 

Mun Shirya Yafewa Masu Yaɗa Bidiyon Batsa A Kafafen Sada Zumunta – Hisba 

Mun Shirya Yafewa Masu Yaɗa Bidiyon Batsa A Kafafen Sada Zumunta - Hisba         Daga Jazuli Zakari Panshekara.

 

 

Hukumar Hisba ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin babban Kwamandan ta Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta ce ƙofar ta a buɗe take ga dukkan masu son tuba daga yaɗa Bidiyon batsa a kafafen sada zumunta.

Babban Muƙaddashin Kwamandan Hisba na jihar Kano Dakta Mujahideen Aminuddeen ne ya tabbatar da hakan a yayin da yake ƙarin haske, dangane da wani sumame da dakarun hukumar suka kai manyan titina da unguwannin jihar domin tabbatar da tarbiyya a tsakanin mutane.

Dakta Mujahideen ya ƙara da cewa, tuni hukumar ta samar da Fom, ga irin waɗannan mutane da suke son tuba kuma su rungumi hanyar shiriya, toh su garzayo hukumar domin su zo ta yafe musu.

A cewar Babban Muƙaddashin Kwamandan, “Dukkan waɗanda suka san sun yaɗa Bidiyon batsa ko na tsiraici a kafafen sada zumunta, kuma suka shirya tuba tun kafin su faɗo hannun hukumar, mun shirya karɓar su domin mu yafe musu”.

Harma ya bada tabbacin cewar hukumar ba ta faɗa da kowa kuma bata neman tada husuma da kowa, illa ƙoƙarin gyara tarbiyyar al’umma musamman waɗanda suka kauce daga kan hanya me kyau.

Daga karshe ya shawarci matasa maza da mata da su kasance masu kulawa rayuwar su ta hanyar Sana’oin dogaro da kai, maimakon shiga wata hanya da zata ɓata sunan su dama na Zuri’ar su gaba-ɗaya.

Wuraran da hukumar ta gudanar da sumamen sune titin Na’ibawa da na gidan zoo, harma da wani wajan shaƙatawa dake cikin unguwar Nasarawa a jihar Kano, a inda ta sami nasarar kama Matasa Maza da Mata masu yawa.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar