Daga Bashir Gasau.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya turawa Majalisar Dattawan Najeriya sunayen Mambobin hukumar gudanarwar sabuwar hukumar nan, ta bunƙasa yankin Arewa maso yammacin Najeriya domin ta tantance su.
Mai bawa Shugaba Tinubu shawara akan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, inda ya ce ci-gaban yazo ne biyo bayan Sanya hannu akan dokar da ta samar da hukumar, a ranar 24 ga watan Yulin da ya gabata.
Mambobin hukumar gudanarwar sune;
(1) Ambasada Haruna Ginsau (Jigawa) – Shugaban Hukumar gudanarwa
(2) Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano) – Manajan Darakta
Sauran Mambobin hukumar gudanarwar sun haɗar da;
(3) Dakta Yahaya Umar Namahe (Sokoto)
(4) Honarabul Aminu Suleiman (Kebbi)
(5) Sanata Tijjani Yahaya Kaura (Zamfara)
(6) Honarabul Abdulkadir S. Usman (Kaduna)
(7) Honarabul Injiniya Muhammad Ali Wudil (Kano)
(8) Shamsu Sule (Katsina)
(9) Nasidi Ali (Jigawa)
A ƙarshe sanarwar ta ce an zaɓo Mutanen ne, domin tabbacin da ake dashi a kansu na ƙwarewa wajen tafiyar da hukumar, ta yadda zai zama hukumar ta ciyar da yankin Arewa maso yammacin Najeriya gaba.