Daga Bello Usman.
Wani rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta ƙasar Argentina ta fitar ya nuna cewa, sama da rabin al’ummar ƙasar na fama da talauci.
Hakan dai na nuna ƙaruwar lamarin daga kashi arba’in cikin ɗari a rubu’i na biyu na shekarar da ta gabata, kuma ya nuna tasirin matakan tsuke bakin aljihu da shugaba Javier Millei ya ɓullo da su.
Tun bayan hawansa karagar mulki a watan Disamba, gwamnati ta rage tallafin da ta ke bayarwa kan sufuri da man fetur da makamashi tare da korar dubban ma’aikatan gwamnati, a ƙoƙarinta na daƙile hauhawar farashin kayayyaki.
Hauhawar farashin kayayyaki a Argentina a cikin watan Agusta, ya kasance ɗaya daga cikin mafi girma a duniya inda ya kai matakin sama da kashi ɗari biyu da talatin.
BBC Hausa