Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja
Sarkin Maraba dake ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa Mista Gambo Allah ya yi, ya tabbatar da naɗin wani ɗan asalin Jihar Kano, Alhaji Musa Saminu (SK), a matsayin Mai Unguwar Abacha Road.
Da yake tsokaci Sarkin Maraba Mista Gambo, ya ce sun naɗa shi ne a sakamakon yadda al’ummar unguwar suka amince dashi, saboda yadda yake zaman lafiya dasu ba tare da nuna bambancin Addini ko na harshe ba.
Suma Al’ummar Unguwar Abacha Road dama na yankin Maraba dake jihar Nasarawar, sun miƙa godiyarsu ga Masarautar Karu da Kuma Sarkin Maraba a bisa naɗin wanda suka amince ya jagorance su.
A nasa ɓangaren sabon mai Unguwar Abacha Road Alhaji Musa Saminu (SK), ya bayyana godiyarsa da wannan dama da al’umma suka bashi, inda yayi fatan zasu bashi haɗin kai domin ya sami damar sauke nauyin da suka ɗora masa.
Hajiya Zainab Musa itace Mai ɗakin sa, tace ƙofar su za ta ci-gaba da kasancewa a buɗe wajen sauraron koken al’umma dama karɓar shawarwari.
A ƙarshe Baturen ‘Yan Sandan dake kula da Abacha road CSP Suleman Ahmad, ya jaddada aniyar sa na ci-gaba da aiki da sarakunan gargajiya da masu unguwanni da ƙungiyoyin Sa-kai, domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Bikin naɗin Sarautar ya sami halartar manyan ‘yan Kasuwa, Ma’aikatan gwamnati, Jami’an tsaro da sauran al’umma.
Unguwar Abacha road dai ta kasance ƙasaitacciyar Unguwar da tafi kusanci da babban birnin tarayya Abuja daga jihar ta Nasarawa.