Daga Aminu Yahaya Tudun Wada.
Hukumar Hisba ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin babban Kwamandan ta Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta sami nasarar kama wata Mata da ta maida gidanta mafakar masu aikata baɗala wato (Lodging).
Babban Muƙaddashin Kwamandan Hisba na jihar Kano Dakta Mujahideen Aminuddeen ne ya tabbatar da hakan a yayin da yake ƙarin haske ga manema labarai, dangane da wani sumame da dakarun hukumar suka kai a Unguwar Titin filin sukuwa.
A yayin sumamen sun kama wasu ‘yan mata masu Ƙananan shekaru da suke taruwa a yankin, a inda masu budurwar Zuciya suke zuwa ɗaukar su suna kaisu Hotel domin aikata baɗala dasu.
A cewar Dakta Mujahideen, “Wani abin baƙin ciki da takaici shine yadda aka sami masu juna biyu dama masu goyo a cikin su, lamarin da yake ƙara fito da illar da hakan ke ƙara haifarwa wannan al’umma”.
Hakan ce kuma ta sanya binciken hukumar ya gano gidan waccan Mata dake unguwar Samaigu a ƙaramar hukumar Kumbotso, wadda ta maida gidan nata mafakar masu aikata baɗala wato (Lodging).
Harma a yayin sumamen bazata da dakarun hukumar suka kai gidan Matar, suka sami Maza Uku da kuma Mata Uku a gidan nata.
Adan haka hukumar ta ce tuni ta fara gudanar da bincike domin gano waɗanda suka bata hayar Gidan, dama ɗaukar matakin Shari’a a kansu ta yadda zasu girbi abinda suka shuka.
A ƙarshe hukumar tayi fatan al’umma zasu ci-gaba da sanya idanu akan dukkan wani shige da ficen dake faruwa a yankunan su, domin kakkaɓe irin waɗannan mutane dake yiwa tarbiyyar al’umma zagon ƙasa.