Daga Bashir Gasau.
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, ya yabawa Gwamnatin jihar Zamfara a bisa irin ƙoƙarin da take yi, wajen magance matsalar tsaron da ke damun sassan jihar.
Sarkin yayi wannan yabo ne, a yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Gwamnatin Jihar a Fadarsa dake Daura, inda ya ce ta cancanci yabo duba da irin faɗi-tashin da suke yi akan al’ummar su, domin ganin an sami zaman lafiya da wadatar arziki a jihar.
A cewar Sarkin Daura, “Jagorancin Dakta Dauda Lawal tare da Muƙarrabansa ya kasance adalin shugabanci, duba da yadda ya kasance masu riƙon amana da kuma addini a yayin jagorancin su”.
A nasa jawabin Shugaban tawagar kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mani Malam Mummuni, ya ce sun je Fadar ne domin neman Tabarrakin Sarkin, da kuma godiya a bisa naɗin Sarautar da aka yiwa ‘yar asalin jihar ta Zamfara.
A cewar Mal Mummuni, “Muna godiya a gareki, a bisa zaɓo wannan ‘yar Gwagwarwa da ta kasance ‘Yar Asalin Jihar Zamfara wato Hajiya Lubna Baba Gusau, kuka bata Sarautar (Gimbiyar Ƙasar Hausa), da fatan Allah ya saka muku da alkhairi”.
Sanarwar da Daraktan yaɗa labaran Muƙaddashin Gwamnan Mika’ilu Muhammad ya aiko wa jaridar GTR Hausa ta ce, dukkan ɓangarorin sunyi fatan Allah ya kawo ɗorewar zaman lafiya a Jihohin Katsina da Zamfara, dama ƙasa baki ɗaya.
Tawagar Gwamnatin jihar ta Zamfara ta ƙunshi Kakakin Majalisar dokokin jihar Zamfara, Rt. Honarabul Bilyaminu Ismail Moriki, Kwamishinan Jin-ƙai, ‘yan Majalisun jihar, da Kantomomin Riƙo na ƙananan Hukumomin Jihar da sauran su.