Daga Bashir Gasau.
Zaki ya kashe wani mai kula da shi a gidan gonar tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Ogun, Omolola Odutola ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce babban jami’in tsaron wurin ne ya kai musu rahoton faruwar lamarin a jiya Asabar.
An bayyana mutumin da suna Babaji Daule mai shekara 35, wanda ɗan asalin jihar Bauchi ne.
“Daga baya an lura cewa mai gadin ya yi sakaci wajen rashin kulle kejin da zakin yake da mukulli kafin ya matsa kusa da shi domin ciyar da shi,” a cewar sanarwar.
Wannan sakacin ne ya sa zakin ya fito kuma ya ji masa raunika a wuya kafin ya rasu daga baya.
Sai da aka harbi zakin kafin ya saki mai gadin, a inda aka kai gawarsa mutuware da ke babban asibitin Ijaye.
BBC Hausa.