Daga Ibrahim Aminu Rimin Kebe.
Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiyar dake aiki da Gwamnatin jihar Kano, sun bayyana aniyar su na tsunduma yajin aikin gargaɗi a ranar 1 ga watan Oktoba me kamawa.
Sakataren ƙungiyar na jihar Kano Dakta Anas Idris Shanono, ne ya sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai, inda ya ce matakin ya zama dole a sakamakon rashin cika musu wasu alƙawura da Gwamnatin Kano tayi.
A cewar Shanono, “Gwamnatin Kano tayi alƙawarin biya mana buƙatun mu tun watan Yuni, amma har yanzu ba ta ɗauki wani mataki na shirin biya mana su ba”.
Alƙawuran da Gwamnatin ta gaza cika wa ƙungiyar sun haɗar da rashin biyansu alawus, tun bayan wucewar annobar Korona, wanda Gwamnatin Tarayya ta biya tun a shekarar 2021.
Sai rashin samun albashi ga sabbin likitocin da aka ɗauka aiki a watan Satumban shekarar 2023.
Haka kuma ƙungiyar ta bayyana damuwar ta, kan rashin isassun likitocin da za su ke duba marasa lafiya a faɗin jihar, inda ta ce jihar Kano me kimanin mutum Milyan 20 amma Likitoci 600 ne kawai suke duba su.
Wanda hakan ke nufin likita ɗaya na kula da marasa lafiya 33,000, tsarin da ya saɓa da ƙa’idar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Bugu da ƙari ƙungiyar ta koka akan yanayin da Asibitocin Jihar suke ciki na rashin manyan kayan aiki.
Adan haka ne ta ce waɗannan sune manyan dalilan da suka sanya suka ɗauki wannan matsaya, domin ankarar da Gwamnati akan buƙatun nasu.