Daga Bashir Gasau.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Yobe, CP Garba Ahmed, ya bada tabbacin bincikar zargin da ake yiwa wani Jami’in su, na kisan wani Matashi bayan wata cacar baki ta shiga tsakanin su.
CP Garba ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya aiko wa jaridar GTR Hausa a yammacin yau Litinin.
Inda ya ce Kwamishinan ya bada umarnin a binciki lamarin Jami’in me suna Sufeto Mohammed Bulama, wanda yake aiki a Barikin ‘Yan Sandan Kwantar da tarzoma me lamba ta 41 dake Damaturun jihar ta Yobe.
A cewar Sanarwar, “A yammacin jiya lahadi ne cacar baki ta haɗa Jami’in namu Mohammed Bulama da wani matashi Abdulmalik Dauda (Baksha) akan wani lamari da ba’a kaiga tantance wa ba.
Kuma bayan faɗa ya kaure ne ake zargin Jami’in ya cakawa matashin Wuƙa a ƙirji, a inda shi kuma Jami’in ɗan Sandan ya ji mummunan rauni a kansa”.
Tuni aka tsare wanda ake zargi domin gudanar da bincike kafin ɗaukar mataki na gaba, harma rundunar ta ce ba zata lamunci irin wannan ɗanyen aiki daga Jami’an nasu ba.
A ƙarshe Kwamishinan ‘Yan Sandan ya yi Allah-Wadai da faruwar lamarin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan Matashin, inda ya basu tabbacin yin adalci akan jinin ɗan uwan nasu.