Home / Government / Mun Shirya Wasan Dambe Domin Murnar Samun ‘Yancin Kai – Kwamared Murtala Gamji

Mun Shirya Wasan Dambe Domin Murnar Samun ‘Yancin Kai – Kwamared Murtala Gamji

Mun Shirya Wasan Dambe Domin Murnar Samun 'Yancin Kai Daga Muhammad Yusif Dambo,Abuja.

 

Shugaban ƙungiyar Dattawan Matasan arewacin Najeriya, Kwamared Murtala Garba (Gamji), ya fara zagayen murnar ranar samun ƴancin kai, wanda ya kasance karo na 64.

Gamji, wanda shine tsohon Shugaban Majalisar Matasa ta ƙasa wato (NYCN), ya fara zagayen ne da shirya wasan damben gargajiya ga ɗaukacin Matasan Arewacin Najeriya, domin murnar zagayowar ranar samun Yancin kan ƙasar.

Toh sai dai duk ya ce gwamnatin ƙasar nan na iya bakin ƙoƙarin ta wajen saita al’amuran tsaro, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu dama dukkan masu ruwa da tsaki a fannin tsaro, su kara ƙaimi akan yadda suka saba na tabbatar da zaman lafiya a arewaci dama Najeriya Baki ɗaya.

Daga ƙarshe ya yi kira ga al’ummar Najeriya baki ɗaya su fito domin nuna goyon bayan su, ga zagayen rangadi da suka fara gudanarwa a Abuja gabanin fafata wasan damben na gobe

Kawo yanzu dai tuni manyan baƙi suka hallara a Babban birnin tarayya Abuja, daga ɗaukacin jihohin Arewacin ƙasar goma, a inda za’a fafata gasar Damben gargajiyar a gobe talata, ranar da ta kasance 1 ga watan Oktoba.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar